logo

HAUSA

Xi Jinping Ya Ziyarci Masu Bayar Da Shawara Kan Harkokin Siyasa

2023-03-06 19:24:27 CMG Hausa

Da yammacin yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ziyarci masu bayar da shawara kan harkokin siyasa da suka fito daga kungiyar masu rajin tabbatar da demokradiyya ta kasar Sin da hadaddiyar kungiyar masana’antu da cinikayya ta kasar, wadanda ke halartar zama na farko na kwamitin majalisar bayar da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 14.

Xi Jinping ya kuma halarci taronsu, inda ya saurari tsokaci da shawarwarin da suka gabatar. (Fa’iza)