logo

HAUSA

Mo Fuyuan, ma'aikacin gidan waya kuma dan majaliar wakilan jama'ar kasar Sin

2023-03-06 16:52:13 CMG Hausa

Malam Mo Fuyuan ke nan, wani ma’aikacin gidan waya da ke lardin Guizhou na kudu maso yammacin kasar Sin, wanda kuma shi ne dan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin. A shekarar 1995, malam Mo Fuyuan, wanda a lokacin ke da shekaru 17 da haihuwa ya kama aikin, kuma a cikin shekarun 28 da suka wuce, ya gane ma yadda ayyukan gidan waya ke dada bunkasa, inda daga keke a farkon fari zuwa motocin da yake amfani yanzu don aikawa da sakwanni, baya ga kuma hanyoyin da aka yi ta gyara.

A matsayinsa na dan majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, Mo Fuyuan ya ce, zai ci gaba da bautawa jama’a, tare da fitar da muryarsu, don ci gaba da samar da gudummawarsa. (Lubabatu)