logo

HAUSA

Tattalin arzikin Sin ya karu da 5.2% kan matsakaicin mataki cikin shekaru 5 da suka gabata

2023-03-05 10:00:32 CMG Hausa

 

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kasar ta samu manyan nasarori a fannin tattalin arziki da zaman takewa cikin shekaru 5 da suka gabata.

Li Keqiang ya bayyana haka ne cikin rahoton aikin gwamnati da ya gabatarwa majalisar wakilan jama’ar kasar a yau Lahadi.

A cewarsa, alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar, sun karu zuwa kudin Sin RMB yuan triliyan 121, kwatankwacin karuwar kaso 5.2 kan matsakaicin mataki cikin shekaru 5 da suka gabata, adadin da ya kai karuwar kusan yuan triliyan 70 cikin shekaru 10 da suka gabata, kimanin kaso 6.2 ke nan kan matsakaicin mataki. Firaministan ya kara da cewa, karfin tattalin arzikin kasar ya karu yadda ya kamata.

A cewar rahoton, cikin shekaru 5 da suka gabata, manufar bude kofa ga ketare da yin gyare-gyare a gida ta kasar Sin ta ci gaba da zurfafa, haka kuma hadin gwiwa karkashin shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya kara karfi, inda darajar kayayyakin da aka yi shige da ficensu ya zarce yuan triliyan 40, lamarin da ya sa kasar Sin ta kasance kan gaba a duniya wajen samun jarin kasashen waje da kuma zuba jari a ketare. (Fa’iza)