logo

HAUSA

Kasar Sin za ta kare hakkokin mallaka na bangarori masu zaman kansu bisa doron doka

2023-03-05 10:15:19 CMG Hausa

 

A cewar rahoton aikin gwamnatin kasar Sin da aka mikawa majalisar wakilan jama’ar kasar domin tattauna kansa, kasar Sin za ta kare hakkokin mallaka na bangarori masu zaman kansu da ma muradu da hakkokin ‘yan kasuwa bisa tanadin doka. Haka kuma za ta ba da goyon baya da kwarin gwiwa ga bangarori masu zaman kansu, tare da taimakawa kanana da matsakaitan masana’antu da daidaikun ‘yan kasuwa, da kuma kyautata dangantaka tsakanin su da gwamnati, gami da samar da kyakkyawan yanayin takara da na ci gaba ga dukkan masana’antu. Bugu da kari, kasar za ta dauki ingantattun matakai na bunkasa kwarin gwiwa da kyakkyawan fata kan yanayin kasuwa. (Fa’iza)