Mata ‘yan sama da shekaru 55 da suke minshari sun kara samun barazanar tsayawar numfashi a lokacin barci
2023-03-05 10:39:31 CMG Hausa
Sabon nazari da aka gudanar a jami’ar Tel Aviv ta kasar Isra’ila ya bayyana cewa, mata ‘yan sama da shekakru 55 da suke minshari sun kara samun barazanar tsayawar numfashi a lokacin da suke barci.
Masu nazari daga jami’ar Tel Aviv sun gudanar da bincike kan darurruwan mata dangane da lafiyarsu, inda suka kwatanta mata ‘yan shekaru 20 zuwa 40 wadanda suke al’ada da kuma ‘yan shekaru fiye da 55 wadanda ba suka daina al’ada. Masu nazarin sun gano cewa, a cikin mata ‘yan shekaru fiye da 55 da suka daina al’ada, wasu kaso 15 suna fuskantar barazanar tsayawar numfashi a lokacin da suke barci, yayin da adadin ya kai kaso 3.5 kawai a cikin mata ‘yan shekaru 20 zuwa 40 da suke da al’ada. Ban da haka kuma, masu nazarin sun gano cewa, a cikin matan da suke minshari, wasu kaso 11 ne suke fuskantar hadarin tsayawar numfashi a lokacin da suke barci, yayin da adadin ya kai kaso 1 kawai a cikin matan da ba sa minshari a lokacin barci.
Masu nazarin suna ganin cewa, sakamakon raguwar yawan sinadarin Hormone a matakin daina al'ada, ya sa mata ‘yan sama da shekaru 55 sun fi saurin gamuwa da matsalar tsayawar numfashi a lokacin barci. Yin minshari kadan har ma mummunar tsayawar numfashi a lokacin barci, dukkansu, matsaloli ne na tsayawar numfashi a lokacin barci, wadanda ke haifar da raguwar iskar oxygen a jinin dan Adam, har ya kai ga mutuwa.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, a yawancin lokaci, mata ba sa son a ce, suna minshari yayin da suke barci. Amma yin minshari, wata muhimmiyar alama ce ta matsalar numfashi a lokacin barci. Idan ba a yin numfashi yadda ya kamata a lokacin barci, kuma ba a je ganin likita cikin lokaci ba, to, zai iya haddasa barkewar wasu cututtuka, kamar shanyewar jiki da matsalar hawan jini da dai sauransu.
Masu nazarin sun kuma ci gaba da cewa, tauna hakora a lokacin barci, yadda mizanin BMI ya wuce misali, da kuma wuya mai kiba, su ma alamun gargadin gamuwa da matsalar tsayawar numfashi a lokacin barci.
Madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, ana minshari a lokacin barci, don haka a yawancin lokaci ba a lura da rashin daidaiton yin numfashi har ma tsayawar numfashi ba, sai dai bayan an farka daga barci, a kan ji gajiya, ko ciwon kai ko kuma ciwon jijiyoyin baka. Ya kamata a je ganin likita cikin hanzari idan a ka ji gajiya ko ciwon kai ko ciwon jijiyoyin baka bayan an farka daga barci. (Tasallah Yuan)