logo

HAUSA

Sin ba abokiyar gabar Amurka ba ce

2023-03-05 21:03:45 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

A kwanakin baya, kwamitocin kula da harkokin diplomasiyya da hada-hadar kudi karkashin majalisar wakilan kasar Amurka sun zartas da wasu shirye-shiryen doka 11 da ke shafar kasar Sin, a yayin da kuma kwamitin musamman mai kula da harkokin takarar Amurka da Sin da majalisar ta kafa ba da jimawa ba, ta gudanar da taron sauraron ra’ayoyin jama’a karo na farko, sai kuma ma’aikatar kula da harkokin wajen Amurka ta zartas da wani shirin da ke da kudin dala miliyan 619 na sayar da makamai da na’urorin soja ga yankin Taiwan na kasar Sin.

Jerin matakan da Amurka ta dauka cike suke da ra’ayoyin yakin cacar baka da ma kiyayya ga kasar Sin, kuma dalilinsu shi ne, don irin ra’ayin da take da shi na cin nasara daga faduwar wani bangare da kuma yadda take daukar kasar Sin a matsayin abokiyar takara mafi kalubale a gare ta. Sai dai daukacin al’ummar Amurka sun san me ke faruwa.

A gun taron kwamitin musamman na kula da harkokin takarar Amurka da Sin karkashin majalisar wakilan Amurka, wata ’yar kungiyar CODEPINK mai rajin kare zaman lafiya ta daga allon da ke dauke da rubutun “Sin ba abokiyar gabanmu ba ce”, don bayyana kyamarsu ga yadda majalisar ta gudanar da irin taron. Malama Jodie Evans na daga cikin wadanda suka kafa kungiyar, kuma ta yi nuni da cewa, ganin yadda karfin kasar Sin ke dada karuwa, mahukuntan Amurka suna yada kararaiyi da ma rura kiyayya ga kasar, a kokarin kiyaye babakeren da suka kafa a duniya. Ta ce, “Abin da muke fatan gani shi ne majalisar wakilan Amurka ta gudanar da irin wannan taro kan zaman lafiya da adalci, a maimakon kiyayya da kuma yaki.”

A hakika, ba a rasa samun Amurkawa da ke da irin wannan ra’ayi. Tuni a lokacin gwamnatin Trump, daruruwan masana da ma mutane daga bangarorin siyasa da kasuwanci suka wallafa wata wasika mai taken “Sin ba abokiyar gabar Amurka ba ce” a jaridar Washington Post, don bayyana rashin amincewa da manufofin gwamnati na yin hamayya da kasar Sin. Tsohon shugaban kasar Amurka, Jimmy Carter, wanda ya gane ma idonsa yadda Sin da Amurka suka kulla huldar diplomasiyya, shi ma sau tari ya bayyana cewa, bunkasuwar kasar Sin ba barazana ba ce.

Sai dai mahukuntan kasar Amurka ba su ji muryoyin ba. Don dakile ci gaban kasar Sin, Amurka da sauran kasashen yammacin duniya sun yi ta yada kalaman nan na wai “Sin barazana ce a duniya”. A hakika, kasar Sin ta cimma ci gaba na zo a gani ta fannoni daban daban,amma ko da gaske ne ci gaban kasar na haifar da barazana?

In mun duba tarihi, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, kasar ba ta taba tada yaki ko rikici ba, kuma ba ta taba mallakar yankunan wata kasa ba, har yanzu kasar ta kasance daya tilo a duniya da ta sanya manufar samun ci gaba ta hanyar lumana cikin kundin tsarin mulkinta. Har kullum kasar na martaba ikon mulkin kai da cikakkun yankunan sauran kasashe, kuma ba ta taba tsoma baki cikin harkokin gidan wasu kasashe ba. Kasashen yammacin duniya na ganin cewa, duk kasar da ta samu karfi, za ta kafa babakere da nuna fin karfi, amma hakan ba zai faru ga kasar Sin ba, sakamakon irin ra’ayoyi na “zama lafiya da juna da martaba bambance-bambance” da “zaman lafiya da kasa da kasa” da “kawar da yake-yake a duniya” da ke cikin al’adun gargajiya na tsawon shekaru sama da 5000 na kasar Sin, ra’ayoyin da a zamanin yau aka bayyana su a cikin shawarar kiyaye tsaron duniya da kasar ta gabatar, wato a rika yin shawarwari a maimakon yin fito na fito, kuma a yi hadin gwiwa a maimakon kulla kawance don mayar da wata kasa saniyar ware, da ma cin moriyar juna a maimakon cin nasara daga faduwar wani bangare.

A ganin kasar Sin, tabbatar da ci gaba yana da muhimmanci wurin warware dimbin matsaloli masu wahala da muke fuskanta a duniya, kuma wannan ne dalilin da ya sa kasar Sin ke sa kaimin hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya, tare kuma da gabatar da shawarar raya duniya. Wani hasashen da bankin duniya ya yi ya nuna cewa, idan aka aiwatar da dukkan ayyukan gina ababen more rayuwa ta fannin zirga-zirga bisa shawarar ziri daya da hanya daya, lallai ya zuwa shekarar 2030, shawarar za ta kawo kudin shiga da ya kai dala triliyan 1.6 a kowace shekara, kuma kasashen da suka amsa shawarar ne za su karbi kaso 90% na kudin.

Don haka, muke iya ganin cewa, bunkasuwar kasar Sin dama ce a maimakon kalubale. Kasar Sin na bunkasa kanta ne ba don wata kasa ba ce, ballantana a ce ta maye gurbin wata, abin da take so kawai shi ne, ta kyautata rayuwar al’ummarta.

Kiyaye kyakkyawar hulda tsakanin Sin da Amurka zai taimaka ga kiyaye moriyar kasashen biyu, har ma da kwanciyar hankali da albarka a duniya baki daya. Sin ba abokiyar gabar Amurka ba ce, kamata ya yi a yi watsi da ra’ayin yakin cacar baka da kuma cin nasara daga faduwar wani bangare, don mayar da huldar da ke tsakanin Sin da Amurka kan hanyar da ta kamata. (Lubabatu)