logo

HAUSA

An bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin

2023-03-05 09:28:10 CMG Hausa

 

An bude zama na farko na taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14 da safiyar yau Lahadi, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping tare da sauran shugabannin kasar na daga cikin wadanda suka halarci bude taron. (Fa’iza)