logo

HAUSA

Sojojin Nijeriya sun ceto wasu fararen hula 14 a yankin arewacin kasar

2023-03-05 11:31:35 CMG Hausa

 

Gwamnatin jihar Kaduna dake arewacin Nijeriya ta ce, dakarunta sun ceto mutane 14 da wasu bata gari suka yi garkuwa da su a jihar.

Wata sanarwar da kwamishinan kula da harkokin cikin gida da tsaro na jihar, Samuel Aruwan ya fitar jiya Asabar, ta ce sojojin Nijeriya ne suka ceto mutanen biyo bayan farmakin da suka kai maboyar bata garin a yankin karamar hukumar Chikun ta jihar a baya-bayan nan.

A cewar sanarwar, dakarun sun ci karfin bata garin, inda suka kashe guda daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere, tana mai cewa, an ceto dukkan mutanen ba tare da sun jikkata ba, haka kuma za a duba lafiyarsu kafin a sada su da iyalansu.

Sai dai kwamishinan bai bayyana ainihin ranar da aka kai farmakin ba, amma ya ce an lalata maboyar bata garin.

Ana samun yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a Nijeriya a watannin baya-bayan nan, lamarin dake kai wa ga mutuwar mutane ko sace su. (Fa’iza Mustapha)