logo

HAUSA

Sin za ta sa kaimi ga samun dinkewar kasa cikin lumana

2023-03-05 10:50:42 CMG Hausa

Bisa rahoton aikin gwamnatin kasar Sin da aka gabatar a yau, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan manufar daidaita batun yankin Taiwan a sabon lokaci, da bin ka’idar “ kasar Sin daya tak a duniya” da ra’ayin da babban yankin Sin da yankin Taiwan suka cimma daidaito kansa a shekarar 1992. Haka kuma, ba za ta amince da ayyukan ‘yan aware ba, inda za ta jajirce wajen raya dangantakar dake tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan da samun dinkewar dukkan sassan kasar cikin lumana.

Game da yankunan Hong Kong da Macau kuwa, rahoton ya yi nuni da cewa, ya kamata a bi manufar “kasa daya amma tsarin mulki biyu”, inda ‘yan Hong Kong da Macau suke aiwatarwa tare da tafiyar da harkokin yankunan biyu da kansu kuma bisa dokoki, da tabbatar da oda bisa kundin tsarin mulkin kasa da dokokin yankunan biyu na musamman. Bugu da kari, za a ci gaba da goyon bayan ayyukan raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama’ar yankunan biyu, tare da tabbatar da zaman lafiya da samun wadata mai dorewa. (Zainab)