logo

HAUSA

Kasar Sin na da burin samun karuwar 5% a GDPnta a 2023

2023-03-05 11:02:17 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce burin ci gaban tattalin arzikin kasar a bana shi ne, GDPnta ya karu da kimanin kashi 5 cikin dari.

Li Keqiang ya bayyana haka ne cikin rahoton aikin gwamnati da ya gabatarwa majalisar wakilan jama’ar kasar a yau Lahadi.

Ban da wannan kuma, Li ya gabatar da sauran burikan ci gaban kasar Sin na bana, wadanda suka hada da, yawan sabbin mutanen da za su samu aikin yi ya kai kimanin miliyan 12, adadin masu zaman kashe wando ya ragu zuwa kaso 5.5 bisa dari, sannan adadin karuwar farashin kayayyakin masarufi ya tsaya kan kaso 3 bisa dari. Kana saurin karuwar yawan kudin shiga da al’ummar Sin za ta samu ya yi daidai da saurin karuwar tattalin arzikin kasar, yayin da za a yi kokarin inganta cinikin shige da fice yadda ya kamata, da kokarin tabbatar da samun daidaito a harkokin cinikin waje. Bugu da kari, kasar Sin za ta yi kokarin cimma burin samar da yawan hatsin da ya wuce kilogiram biliyan 650, da rage amfani da kwal, man fetur, iskar gas, tare da ci gaba da kyautata muhallin halittu.(Kande Gao)