logo

HAUSA

Kotun kolin Najeriya ta bayar da umarni a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira

2023-03-04 16:12:21 CMG Hausa

A jiya ne, kotun kolin Najeriya ta bayyana cewa, dokar da babban bankin Najeriyar wato CBN ya aiwatar game da maye gurbin tsoffin takardar kudin kasar wato Naira da sabbi ya saba doka.

A watan Oktoban shekarar 2022 ne, babban bankin Najeriyar ya fito da sabbin takardun kudin Naira da aka sauyawa fasali, da fatan shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki da kuma dakile halasta kudaden haram.

A ranar 3 ga watan Fabrairu kuma, jihohin Kaduna,da Kogi da Zamfara dake tarayyar Najeriya, suka shigar da kara a gaban kotun kolin kasar, domin kalubalantar aiwatar da manufar. Tun a wancan lokaci ne kuma, gwamnatocin jihohin Najeriya 13 ne suka shiga shari'ar, a matsayin masu shigar da kara, inda suka ce manufar tilasta maye gurbin toffin takardun kudin da sabbi cikin kankanin lokaci, ya cusa 'yan Najeriya cikin tsananin matsala.(Ibrahim)