logo

HAUSA

Mutane 12 sun gamu da ajalinsu sakamakon fashewar bututun mai a kudancin Najeriya

2023-03-04 15:51:34 CMG Hausa

Rundunar ‘yan sandan jihar Rivers dake kudancin Najeriya ta bayyana cewa, a kalla mutane 12 ne suka mutu da sanyin safiyar Juma'ar da ta gabata, sakamakon fashewar wani bututun mai a jihar Rivers da ke kudancin kasar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, fashewar da ta auku a yankin Rumuekpe da ke karamar hukumar Emuoha ta jihar Rivers, ta faru ne a daidai lokacin da mazauna yankin ke kwasar mai daga bututun da ya ratsa yankin al’ummar. (Ibrahim)