logo

HAUSA

NPC ta gudanar da taron manema labarai gabanin bude taron shekara-shekara

2023-03-04 17:05:57 CMG Hausa

Da safiyar yau ne, majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC), dake zama babbar majalisar tsara dokokin kasar, ta gudanar da taron manema labarai, gabanin bude taronta na shekara-shekara.

Da misalin karfe 9 na safiyar gobe Lahadi ne, aka tsara za a bude taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 14, kana za a kammala shi a ranar 13 ga wata, kamar yadda mai magana da yawun taron, Wang Chao, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

A cewar Wang, baya ga nazarin jerin rahotanni da suka hada da rahoton aikin gwamnati, ana saran wakilan NPC za su tattauna kan daftarin shirin gyaran dokar kafa dokoki da kuma shirin yin garambawul ga hukumomin majalisar gudanarwar kasar.

Wang Chao ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka, kan inganta tsarin doka game da kara bude kofa ga kasashen ketare, bugu da kari, kasar Sin ta kudiri aniyar ciyar da sha’anin doka gaba a fannin kiyaye muradun ikon mulkin kasa da tsaro, da samun bunkasuwa.

Wang Chao ya kara da cewa, kasar Sin ba ita ce kasar da ta fi kowacce kasa bayar da bashi ga kasashen Afirka ba, kamar yadda alkaluma daga bankin duniya suka nuna cewa, kusan kashi uku bisa hudu na bashin da ake bin kasashen Afirka, sun fito ne daga cibiyoyin hada-hadar kudi mallakar bangarori daban daban da masu lamuni na kasuwanci. Wang Chao ya ce, har kullum kasar Sin ta himmatu wajen taimakawa kasashen Afirka rage bashin da ake bin su, yana mai karyata ikirarin cewa, wai kasar Sin na haifar da abin da ake kira "tarkon bashi" a Afirka. (Ibrahim)