logo

HAUSA

Lionel Messi ya zama gwarzon dan kwallon duniya na hukumar FIFA na shekarar 2022

2023-03-03 15:23:54 CMG Hausa

An gudanar da bikin mika lambobin yabon hukumar hadin gwiwar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA a birnin Paris na Faransa a ranar 27 ga watan Febrairu, dan wasan gaba kuma kyaftin din kungiyar kasar Argentina Lionel Messi ya cimma lambar yabo na gwarzon dan kwallon duniya na hukumar FIFA na shekarar 2022 ajin maza, kana kungiyar Argentina ta fi samu lambobin yabo a gun bikin a wannan karo.

Messi ya samu irin wannan lambar yabo a karo na baya wato a shekarar 2019, kuma a shekarar 2020 da kuma ta 2021, dan wasan kungiyar kasar Poland Robert Lewandowski shi ma ya cimma wannan lambar yabo. Messi, wanda shi ne kyaftin din kungiyar kasar Argentina da ta lashe kofin duniya na FIFA a bara a kasar Qatar, bayan doke Faransa a wasan karshe da ya yi matukar kayatarwa, ya samu lambar yabon a wannan karo.

Kungiyar Argentina ta samu lambobin yabo guda hudu a gun bikin a wannan karo domin ta yi wasa mai kayatarwa a gun gasar cin kofin duniya ta kasar Qatar ta shekarar 2022. Ban da Messi, mai horaswa na kungiyar Argentina Lionel Scaloni ya lashe lambar yabo na kociya mafiya kwarewa, kana dan wasan bugu daga kai sai mai tsaron gida na kungiyar Argentina Emiliano Martínez ya lashe lambar yabo na gwarzon dan wasan bugun daga kai sai mai tsaron gida na hukumar FIFA na shekarar 2022, da kuma dukkan masu sha’awar wasan kwallon kafa na kasar Argentina sun samu lambar yabo na masu sha’awar wasan mafi kyau na duniya na shekarar.

‘Yar wasan Sifaniya Alexia Putellas ta samu lambar yabo na gwarzon ‘yar kwallon duniya na hukumar na shekarar 2022 ajin mata, wannan ne karo na biyu da ta samu irin lambar yabo a jere. Ita ma ta lashe kyautar Ballon d'Or ajin mata a shekaru biyu da suka gabata a matsayin ‘yar wasan kungiyar Barcelona ta kasar Sifaniya.

Ban da wannan kuma, Sarina Wiegman, mai horaswa ta kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Ingila ta lashe lambar yabo ta kociya mace mafi kwarewa, inda ta jagoranci kungiyar mata ta Ingila da ta lashe gasar UEFA European Football Championship ajin mata ta shekarar 2022, kana dan wasan nakasassu na kasar Poland Marcin Oleksy ya samu lambar yabo ta zura kwallo mafi kayatarwa ta shekarar 2022, domin ya zura kwallo daya mai kayatarwa a gasar wasan kwallon kafa ta nakasassu a watan Nuwanbar shekarar bara, wanda ya burge masu sha’awar wasan kwallon kafa na duniya sosai.

Marigayi mashahurin dan wasan kwallon kafa na kasar Brazil Pelé ya samu lambar yabo ta musamman da hukumar FIFA ta bayar, shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino da tauraron dan wasan kwallon kafa na kasar Brazil Ronaldo Luiz Nazario sun bayar da lambar yabo ga iyalin Pelé.

 

Kungiyar wasan kwallon kafa ta Argentina ta tsawaita kwangilar mai horaswa Lionel Scaloni

 

Kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Argentina ta sanar a kwanakin baya cewa, za ta tsawaita kwangilar mai horaswa Lionel Scaloni har zuwa shekarar 2026.

Scaloni ya jagori kungiyar Argentina da ta lashe gasar cin kofin duniya ta kasar Qatar, inda Argentina ta sake daukar kofin bayan shekaru 36.

Scaloni mai shekaru 44 da haihuwa ya taba zama dan wasan kungiyar Argentina, da shiga jerin sunayen membobin kungiyar Argentina da ta halarci gasar cin kofiin duniya ta shekarar 2006.

Bayan gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018, Scaloni ya zama mai horaswa na kungiyar Argentina. A shekarar 2021, kungiyar Argentina da ya jagoranta ta doke kungiyar Brazil da cin kofin nahiyar Amurka, don haka ya kawo karshen gaza cimma zakara da kungiyar Argentina ta yi har na tsawon shekaru 28.

 

Aleksandar Jankovic ya zama sabon mai horaswa na kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ajin maza

 

Hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta sanar a kwanakin baya cewa, dan kasar Serbia mai shekaru 50 da haihuwa Aleksandar Jankovic ya zama sabon mai horaswa na kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ajin maza.

Hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, don share fagen gasar cin kofin Asiya ta shekarar 2023 da gasar neman samun iznin shiga gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 ta yankin Asiya, rukunin masana a wannan fanni na kasar Sin ya yi tattaunawa da bada shawara, inda hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta yi nazari da zartas da shawarar, da tsaida kudurin nada Jankovic a matsayin mai horaswa na kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin.

An haifi Jankovic a watan Mayu na shekarar 1972, kafin wannan, ya taba zama mai horaswa na kungiyar ‘yan kasa da shekaru 21 da haihuwa wato U21 ta wasan kwallon kafa ta kasar Serbia, da kuma na kungiyoyi da dama na kasashen Turai, kana ya taba lashe lambar yabo ta mai horaswa mafi hangen nesa na kasar Serbia na shekarar 2011 da hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar ta bayar.

A watan Satumba na shekarar 2018, Jankovic ya zama mai horaswa na kungiyar ‘yan kasa da shekaru 19 da haihuwa wato U19 ta wasan kwallon kafa ta kasar Sin. A shekarar 2020, shi ya ci gaba da sa hannu kan kwangilar zama mai horaswa na kungiyar U21 don share fagen gasar wasanni ta Asiya ta birnin Hangzhou. A watan Yuli na shekarar 2022, ya jagori yawancin ‘yan wasan U23 na kasar Sin da halartar gasar cin kofin gabashin Asiya da aka gudanar a kasar Japan, kuma kungiyar ta cimma nasara 1 da kunnen doki 1 da cin tura 1, inda ta zama a matsayi na uku a karshe.

A matsayin sabon mai horaswa na kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin, wasa na farko da Jankovic zai jagoranci kungiyar ta buga shi ne gasar wasan kwallo ta sada zumunta tsakanin Sin da New Zealand a ranar 23 ga wannan wata a birnin Oakland.

 

Za a kaddamar da gasar cin kofin Asiya ta shekarar 2023 a watan Janairu na shekarar 2024

 

Hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Qatar ta sanar a ranar 28 ga watan Febrairu cewa, za a gudanar da gasar cin kofin Asiya ta hukumar hadin gwiwar wasan kwallon kafa ta Asiya ta shekarar 2023 tun daga ranar 12 ga watan Janairu zuwa ranar 10 ga watan Febrairu na shekarar 2024.

Kana hukumar kula da harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Qatar ta sanar da kafa kwamitin kula da gasar cin kofin Asiya ta kasar Qatar, inda kungiyoyin wasan kwallon kafa guda 24 ciki har da kungiyar kasar Sin za su halarci gasar a wannan karo.

A watan Oktoba na shekarar 2022, kwamitin gudanarwa na hukumar hadin gwiwar wasan kwallon kafa ta Asiya ya jefa kuri’a, da tsaida kudurin zabar kasar Qatar a matsayin wurin da za a gudanar da gasar cin kofin Asiya ta shekarar 2023. Wannan zai kasance karo na uku da kasar Qatar ta gudanar da gasar cin kofin Asiya bayan shekarar 1988 da kuma ta 2011. (Zainab Zhang)