logo

HAUSA

Me ya sa "Fitilar hakkin bil’adam" ba ta haskaka yara ma'aikata masu gwagwarmaya a kasa ba?

2023-03-03 21:18:06 CMG Hausa

Yara su ne fata da makomar duniya. Sai dai wani rahoton da kungiyar kwadago ta kasa da kasa da asusun kula da kananan yara na MDD suka fitar a farkon watan Maris ya nuna cewa, har yanzu yara na fama da matsalar talauci mai tsanani, inda aka yi kira ga kasashen duniya da su kara kare yara. Game da wannan kira, Amurka, wacce ke ikirarin ita ce "Fitilar hakkin bil’adam", musamman ya kamata ta saurari wannan kira.

Bisa alkaluman da ma'aikatar kwadago ta Amurka ta fitar, a cikin kasafin kudi na shekarar 2022, yawan yara da kamfanoni 835 a fadin Amurka suka dauka aiki, ya kai fiye da 3800 ba bisa doka ba, wanda ya karu da fiye da 1000 bisa shekarar da ta gabata.

Bugu da kari, kamar yadda cinikin bayi da nuna bambanci ga kabilu, batun yaran dake aiki a Amurka yana da dogon tarihi. Tun fiye da shekaru 100 da suka gabata, wurin hakar ma'adanai, gonakin taba, da masana'antun saka tufafi na Amurka sun fara daukar ma'aikatan yara. Har illa yau, har yanzu ba a warware wannan batu ba, muhimmin dalili shi ne kura-kuran dake cikin tsarin shari'ar Amurka da rashin aiwatarwa.

Mummunan yanayi da ma’aikata yara suke ciki, shi ne daya daga cikin batun cin zarafin hakkin yara a Amurka. A halin yanzu, Amurka ita ce mamba daya tilo ta MDD da ba ta zartas da "Yarjejeniyar Kare Hakkin Yara" ba. Kungiyar kwadago ta duniya ta sha sukar Amurka kan batun yanayi mai tsani da ma’aikata yara ke ciki a kasar, kasashen duniya kuma sun yi Allah wadai da ita, a matsayin "babban mai cin zarafin hakkin dan Adam".

Lokacin da yara suka daina muradin "Mafarkin Amurka", wane kwarin gwiwa da gwamnatin Amurka take da shi wajen yin alfahari da kasancewa "Fitilar kare hakkin dan Adam"?(Safiyah Ma)