Hadin gwiwar Sin da IMF zai taimakawa duniya shawo kan kalubalen da take fuskanta
2023-03-02 11:47:56 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ce, yayin da ake fuskantar matsaloli a yanayin shiyyoyi da ma duniya, dangantakar abota tsakanin Sin da asusun bada lamuni na duniya (IMF), ba bangarorin biyu kadai zai yi wa amfani ba, har ma da al’ummomin duniya baki daya, ta hanyar hada hannu domin shawo kan kalubalen da duniya ke fuskanta.
Li Keqiang ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa ta wayar tarho da manajan daraktar bankin, wato Kristalina Georgieva.
A cewar Li Keqiang, kasar Sin ce kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kuma mai ingiza hadin gwiwar kasashe masu tasowa, haka kuma, ta kuduri niyyar cike gibin dake akwai tsakanin kasashe masu arziki da masu tasowa.
Firaministan na kasar Sin, ya ce magance matsalolin bashin dake kan kasashe masu karancin kudin shiga, na bukatar gudunmawar dukkan masu bayar da bashin, kuma Sin ta shirya taka rawa wajen warware matsalolin basussukan wadancan kasashe ta hanyar wani tsari na hadin gwiwa.
Ya kara da cewa, Sin na bukatar dukkan bangarorin da batun ya shafa su hada hannu su raba nauyin bisa adalci da oda, domin taimakawa kasashen shawo kan kalubalen tattalin arziki da samun ci gaba mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)