logo

HAUSA

Dakarun gwamnatin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab sama da 200

2023-03-02 11:53:13 CMG Hausa

Dakarun gwamnatin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab sama da 200, ciki har da shugabannin kungiyar, yayin wani farmaki na tsawon kwanaki 3 da suka kai sassan tsakiya da kudancin kasar.

Ministan yada labarai da raya al’adun da yawon bude ido na kasar Daud Aweis, ya bayyana a jiya cewa, jami’an tsaro sun ’yantar da sabbin yankuna a jihohin Hirshabelle da Galmudug da Jubaland, inda suka kashe adadi mai yawa na masu ikirarin jihadi.

Daud Aweis ya kara da cewa, jami’an tsaro da suka samu goyon bayan takwarorinsu na kasashen waje, sun yi nasarar kai farmaki a fagen daga a jihohi kamar na Banadir da Hirshabelle da South West da Jubaland da Galmudug, domin zakulo mayakan dake arangama da dakarun gwamnati a kusan kullum.

Ministan ya ce a kokarinsu na karfafa tsaro a babban birnin kasar, har ila yau, jami’an tsaro sun cafke ’ya’yan kungiyar al -Shabab 3, wadanda ke shirya wasu hare-hare.

Ya kara da cewa, kwamitin tsaro na MDD ya yi maraba da wannan nasara da gwamnati ta samu yakin da take da kungiyar al-Shabab a kasar, da kuma nasarorin da aka samu wajen tabbatar da kyautatuwar dangantaka da hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasa da ta jihohi. (Fa’iza Mustapha)