logo

HAUSA

Kalubalolin da Mista Bola Tinubu zai fuskanta

2023-03-02 11:33:45 CMG Hausa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Najeriya ta sanar a jiya Laraba cewa, dan takarar jam’iyyar APC Bola Tinubu ya lashe babban zaben da ya gudana a kasar a ranar 25 ga watan Fabrairu, inda ya zama zababben shugaban kasar Najeriya. A ganin manazarta al’amuran duniya, bayan da Mista Tinubu ya hau kujerar mulki, zai fuskanci kalubale, a fannin daidaita wasu matsaloli 2 da kasarsa ke fuskanta, wato koma-bayan tattalin arziki, da yawan abkuwar hare-hare.

An ce, yawan kuri’un da Mista Tinubu ya samu ya fi na Atiku Abubakar, dan takarar zaben shugabancin kasa da ya zama na biyu, da kuri’u fiye da miliyan 1 da dubu dari 8. Amma a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya sake cin zabe a shekarar 2019, yawan kurin’un da ya samu ya wuce na mai matsayi na biyu da wasu fiye da miliyan 3 da dubu dari 9. Ta haka za mu iya ganin alamar raguwar fifikon da dan takarar jam’iyya mai rike da ragamar mulki ke samu. Wannan yanayi, a cewar masu nazarin al’amuran duniya, zai zama matsin lamba ga Mista Bola Tinubu, don ya yi kokarin biyan bukatun jama’ar kasar a harkokin da suke jan hankalinsu, irin su tattalin arizki, da zaman rayuwa, gami da harkar tsaro.

A ganin Farfesa Sheriff Ghali, mai nazarin ilimin siyasa da huldar kasa da kasa na jami’ar Abuja ta Najeriya, Mista Tinubu zai fi fuskantar kalubaloli a fannin zaman rayuwar al’umma, wadanda suka hada da matsalar talauci, da rashin guraben aikin yi, da hauhawar farashin kayayyaki, da karancin kudin musaya, da wutar lantarki, da dai makamantansu.

A cewar Farfesa Ghali, Najeriya na fuskantar yanayin tsaro mai tsanani, ya ce ko da yake sojojin kasar suna ta daukar matakai don neman dakile kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi, da ‘yan fashi, amma ana ci gaba da samun abkuwar hare-hare a wurare daban daban na kasar. Matsalar rashin tsaro a kasar Najeriya wani batu ne mai sarkakiya, wanda ya dade yana ci wa al’ummar kasar tuwo da kwarya, sai dai neman daidaita shi ba aiki ne mai sauki ba. Saboda haka ana bukatar Mista Tinubu ya dauki karin ingantattun matakai masu amfani a nan gaba, in ji Farfesa Ghali. (Bello Wang)