Sin ta musanta kalaman da Blinken ya yi kan Sin
2023-03-02 20:44:58 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin waje Sin Mao Ning ta musanta kalan da sakataren harkokin wajen Amurka Blinken kan Sin a gun taron manema labarai da aka saba yi yau Alhamis, inda ta bayyana cewa, a kan batun Ukraine, bangaren Sin ya tsaya tsayin daka kan matsayi na nuna adalci, ya kuma himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya, inganta warware rikicin siyasa, ya kuma dade yana bangaren zaman lafiya da tattaunawa. Amurka ta dade tana aike muggunan makamai zuwa fagen daga na Ukraine, tare da rura wuta da yada labaran karya a ko’ina, kasar Sin tana matukar adawa da hakan.(Safiyah Ma)