logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya Nikos Christodoulides murnar zama sabon shugaban kasar Cyprus

2023-03-01 10:44:10 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga Nikos Christodoulides domin taya shi murnar rantsar da shi a matsayin shugaban kasar Cyprus.

Shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a halin yanzu, an kiyaye raya dangantakar dake tsakanin Sin da Cyprus, da sada zumunta na dogon lokaci, da yin imani da juna a harkokin siyasa, da kara yin hadin gwiwa a fannoni daban daban a tsakaninsu. Kasar Sin tana dora muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Cyprus, kana shugaba Xi Jinping yana son hada kai tare da Christodoulides don sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu don amfanawa jama’arsu baki daya. (Zainab Zhang)