Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na Belarus
2023-03-01 21:40:28 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Belarus, Alexander Lukashenko, yau Laraba a birnin Beijing.
Yayin ganawar, Xi Jinping ya ce duniya na fuskantar manyan kalubale da aka dade ba a gani ba, kuma akwai jan aiki na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya. Ya ce Sin da Belarus sun kasance masu muradi iri guda ta fuskar tabbatar da adalci da daidaito a duniya. Kuma Sin na yabawa goyon bayan da Belarus ke bata kan shawarar raya duniya da ma shawarar kiyaye tsaron duniya da ta gabatar. Ya kara da cewa, a shirye Sin take ta karfafa hadin gwiwa da Belarus a dandalin MDD da ma na sauran hukumomin kasa da kasa, wajen shawo kan kalubalen da duniya ke fuskanta da gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama.
A nasa bangare, shugaba Alexander Lukashenko, ya ce kasar Sin ce jigo wajen kiyaye tsaron duniya. Kuma a shirye Belarus take ta karfafa hadin gwiwa da Sin kan muhimman batutuwan da suka shafi duniya da shiyyoyi da hada hannu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.
Shugabannin biyu sun kuma tattauna kan rikicin Ukraine da sauran batutuwa.