logo

HAUSA

Hukumar zabe a tarayyar Najeriya ta sanar da sakamakon karshe na shugaban kasa

2023-03-01 16:08:18 CMG Hausa

Da asubahin ranar Laraba 1 ga watan Maris shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu ya sanar da sakamakon karshe na ’yan takarar shugaban kasa, inda ya ayyana Bola Ahmed Tinubu mai shekaru 71 a matsayin mutumin da ya samu nasara.

Bola Ahmad Tinubu dan jam’iyyar APC mai mulkin kasar a yanzu ya samu nasara ne da kuri’u miliyan 8,794,726 a kan sauran abokan takarar sa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

’Yan takara 18 ne suka fafata a zaben shugaban kasar na ranar Asabar 25 ga watan jiya ciki har da Tinubu.

A loakcin da yake sanar da sakamakon zaben Farfessa Mahmud Yakubu ya ce Bola Tinubu ya cike dukkan sharudan da doka ta tanadar na kasancewa mutumin da ya yi nasara a kan sauran takwarorin sa 17 inda ya samu kuri’u mafi rinjaye.

Ya ce dan takarar na jam’iyyar APC ya kai ga samun kaso 25 na adadin yawan kuri’un da aka kada a jahohi 30 na kasar.

Shugaban hukumar zaben ta tarayyar Najeriya ya ci gaba da cewa mutumin da ya zama na biyu shi ne dan takarar jam`iyyar PDP  Alhaji Atiku Abubakar da kuri’u miliyan 6,984,520, sai Peter Obi na jam’iyyar Labour Party da ya samu kuri’u miliyan 6,101,533 yayin da Dr Rabi’u musa Kwankwaso na jam`iyyar NNPP ya samu kuri u miliyan 1,496,687.

INSERT…………..

Dukkanin ’yan takarar 4 kamar yadda shugaban hukumar zaben ya bayyana sun samu nasara a kalla jiha daya, inda Tinubu da Atiku da Peter Obi suka samu nasara a jahohi 12 kowannen su yayin da Kwankwaso ya samu nasara a jiha 1.

Jahohin da Bola Tinubu ya samu nasara sun hada da Rivers, Borno, Jigawa, Zamfara, Bunue, Kogi, Kwara , Niger, Osun, Ekiti, ondo, Oyo da kuma Ogun.

Shi kuma Atiku Abubakar ya samu nasara a jahohin Katsina Kebbi, Sokoto, Kaduna, Gombe,Yobe, Bauchi, Adamawa, da Taraba.

Mr Peter Obi ma jam`iyyar Labour ya ci jahohin Edo, Cross rivers, Delta, Legos, Plato, imo Ebonyi, Nasarwa, Anambra, Abia, Enugu da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Yayin da shi kuma Dr. Rabi u Musa Kwankwaso ya samu nasara a jihar Kano.

A jawabin sa bayan samun nasara, zababben shugaban tarayyar Najeriya mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu, ya ce yana godiya da tare da farin cikin kasancewar sa shugaban tarayyar Najeriya na 16 tun bayan samun ’yanci.

Daga nan kuma ya yi kira ga abokanann takarar sa.

“Zan yi amfani da wanann dama na bukaci dukkan wadanda mukayi takara tare da su za mu hada kai mu gina kasar mu, ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya wajibi ne mu taro mu bunkasa ta.”

Yan haka dai magoya bayan jam`iyyar ta APC na ci gaba da gudanar da murnar samun nasara a zaben shugaban kasa mafi daukar hankalin kasashen duniya. (Garba Abdullhi Bagwai)