Kasar Sin: EU ta keta ka’idojin kasuwa bisa hana amfani da TikTok a na’urorin aiki
2023-03-01 20:16:47 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta bayyana adawa da matakin Tarayyar Turai na haramta amfani da manhajar TikTok a kan wayoyin salular ma’aikatan gwamnati. Inda ta ce ci gaba da kuntatawa kamfanonin kasashen waje bisa fakewa da tsaron kasa, illa zai yi ga kwarin gwiwar da kasa da kasa ke da shi a muhallin kasuwanci.
Kakakin ma’aikatar Mao Ning wadda ta bayyana hakan, ta ce kamata ya yi EU ta girmama ka’idojin kasuwa ta daina yi wa batun tsaron kasa kudin goro, kuma ta samar da yanayi mai kyau ga kamfanonin kasashen waje.
