logo

HAUSA

Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon shugaban kasar Nijeriya

2023-03-01 14:05:38 CMG Hausa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta sanar da sanyin safiyar yau cewa, dan takarar jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben shugaban kasar Nijeriya da aka yi a ranar 25 ga watan Febrairu.

A ranar 26 ga watan Fabrairu ne, hukumar ta fara kidaya kuri’u a cibiyar taron kasa da kasa dake birnin Abuja, babban birnin Najeriya. Sakamakon karshe ya nuna cewa, a cikin dukkan kuri’u fiye da miliyan 24 da aka kada, Tinubu ya samu fiye da kuri’u miliyan 8 da dubu 790, dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya samu kuri’u miliyan 6 da dubu 980, yayin takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi ya samu kuri’u miliyan 6 da dubu 100. (Zainab Zhang)