logo

HAUSA

Sin ta bukaci Amurka da ta daina batanci ga jam’iyyar kwaminis ta Sin

2023-03-01 20:40:48 CMG Hausa

A kwanan nan, kwamitin musamman kan batun kasar Sin na majalisar wakilan Amurka ya gudanar da taron sauraron ra’ayin jama’a game da abun da ya kira “barazanar jam’iyyar kwaminis ta Sin ga Amurka”. Dangane da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning ta bayyana yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau Laraba cewa, bangaren Sin na bukatar hukumomi da ma’aikatun Amurka masu ruwa da tsaki, su bar bambancin akida da tunanin yakin cacar baka, su kalli dangantakar Sin da Amurka bisa gaskiya da hankali, su daina yada “ra’ayin barazanar Sin” bisa bayanan karya. Haka kuma, su daina batanci ga jam’iyyar kwaminis ta Sin, kuma su daina garkuwa da dangantakar Sin da Amurka don yunkurin samun moriyar siyasa.

Ban da wannan, yayin da take ba da amsa kan tambayar da aka yi game da maganganu na kuskure da hukumar FBI ta Amurka ta yi game da asalin kwayoyin cutar COVID-19, Mao Ning ta jadadda cewa, bangaren Sin yana adawa da siyasantar da batun asalin kwayoyin cutar. Tana mai cewa, Sin ta dade tana bada goyon baya da kuma shiga aikin lalubo asalin kwayar cutar COVID-19 ta hanyar kimiyya, inda ta ce nemo asalin kwayoyin cutar batu ne na kimiyya mai tsanani, kuma kamata ya yi masana kimiyya na kasa da kasa su yi hadin gwiwa don gudanar da bincike.(Safiyah Ma)