logo

HAUSA

Xi Jinping ya damu da gadon al’adun kasar Sin(8) Al'adun gargajiya masu armashi

2023-02-28 21:58:42 CRI

“Manas” da “Gesar” da “Jangar” wasu muhimman almara 3 ne na kasar Sin. Sun samo asali ne daga tatsuniyoyin kabilun Tibet da Kirgiz da Mongoliya, kuma Sakatare Janar na kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya sha ambatonsu a lokuta da dama.

Al’adun kasar Sin sun kunshi al’adun kabilu daban-daban. A cewar Xi Jinping, “cudanyar al’adun dukkan kabilu da dadewa da ingantuwarsu, su ne tushen kwarin gwiwar da muke da shi kan al’adunmu”.