logo

HAUSA

Kasashen Nijar da Libiya na kokarin kyautata huldar dangantarkarsu

2023-02-28 09:42:37 CRI

Tun bayan mutuwar shugaban kasar Libiya, Mohammouar Khaddafi, kasar ta fada cikin wani rikicin siyasa, wanda kuma hukumomin kasar masu ci a yanzu haka suke kokarin maido da zaman lafiya da tsarin demokuradiyya cikin wannan kasa, dalilin ke nan ministan dake kula da harkokin matasa na kasar Libiya, kana kuma manzon musammun na faraministan kasar Libiya, Fathallal Al-Zouni ya sauka birnin Yamai na kasar Nijar a ranar jiya da yamma, 27 ga watan Febrairun shekarar 2023 domin ganawa da shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum.

Daga saukarsa a filin jirgin sama na kasa da kasa na Diori Hamani, ministan matasan kasar Libiya, kuma manzon musamman na firaministan kasar Libiya Fathallal Al-Zouni ya isa fadar shugaban kasar Nijar dake nan birnin Yamai. A yayin tattaunawar tasu, shugaba Mohamed Bazoum da bako nasa sun maida hankali kan batun karfafa dangantakar makwabtaka, da zumunci dake tsakanin kasashen Nijar da Libiya, haka kuma da ingiza ayyukan kungiyar CEN-SAD.

“Mun roki, Mohamed Bazoum, a matsayinsa na shugaban kasa makwabciya mai zaman lafiya kuma da demokuradiyya da ya yi amfani da tunaninsa da kwarewarsa domin maido da dukkan ’yan kasar Libiya kan teburi guda domin tattaunawa, da kuma amfani da karfinsu da ra’ayoyinsu domin taimakawa Libiya shiga hanyar demokaradiyya da cigaba”, in ji ministan kasar Libiya.

Haka kuma, wakilin faraministan Libiya, ya kuma bukaci shugaban kasa Bazoum Mohamed da ya taimakawa kungiyar CEN-SAD shirya taronta na shugabanni da gwamnatoci, da aka kwashe shekaru 4 ba a gudanar da irin taron ba.

Daga karshe, shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya tabbatarwa babban bakonsa cewa zai yi amfani da niyyarsa da kuma matsayinsa wajen taka rawar da ya kamata domin ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali sun sake tabbata a kasar Libiya domin moriyar kasashen biyu dake makwabtaka da juna da kuma ci gaban nahiyar Afrika baki daya.

Haka zalika, shugaba Mohamed Bazoum ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen amfani da karfinsa da kuma kwarewarsa domin ganin kungiyar SEN-SAD ta dawo da martabobinta na ci gaba kasashen Afrika da ma duniya.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.