logo

HAUSA

Xi Jinping ya damu da gadon al’adun kasar Sin(7) Dukiyar tsibirin Egret

2023-02-28 21:53:42 CRI

A watan Satumban 2017 an gudanar da taron kasashen BRICS da suka hada da Brazil da Rasha da India da Sin da Afrika ta kudu, a birnin Xiamen. Yayin liyafar maraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da birnin a matsayin inda ya taba aiki. “Xiamen dake da kyan gani da yanayi mai armashi, fitaccen wuri ne dake bakin teku a kasar Sin. A watan da ya gabata, Kulangsu, wani karamin tsibiri da ake wa lakabi da “wurin adana kayayyakin tarihi na gine-gine” da kuma “mazaunin baki ‘yan kasashen waje” ya shiga cikin jerin abubuwan gado na duniya, lamarin da ya kara haskaka birnin.