logo

HAUSA

Laifi tudu, ka hau naka ka hango na wani

2023-02-28 20:06:00 CMG Hausa

Kasar Sin ta bayyana adawarta da matakin Amurka na kakabawa wasu kamfanoninta takunkumi bisa dalilai masu nasaba da rikicin Rasha da Ukraine.

Hausawa kan ce, laifi tudu ne ka hau naka ka hangi na wani. Abu ne da kowa ya sani cewa, Amurka ita ce ta ingiza Ukraine shiga halin da take ciki yanzu haka, haka kuma, ita da kawayenta ne ke ci gaba da ruru wutar wannan rikici da ya shafe shekara guda ana yi.

Amma sai ta gaza ganin laifinta na zuba makudan kudi har sama da dala biliyan 46 wajen samar da makamai ga kasar Ukraine, wadanda za a yi amfani da su wajen haifar da asara da illa, maimakon karkatar da su ga abubuwan da al’umma za su amfana, inda take neman shafawa kasar Sin bakin fenti. Kasar Sin din da ta tsaya tsayin daka wajen kaucewa daukar bangare a rikicin, inda ta nace cewa, hanya mafi dacewa ita ce tsagaita bude wuta da hawa teburin sulhu.

Amurka ta yi gaban kanta wajen kakabawa kamfanonin Sin takunkumi, matakin dake nuna yadda kasar ke nuna isa da danniya da kokarin babakere a duniya, domin kakaba takunkuman ba huruminta ba ne, kana bai samu goyon baya ko sahalewar kwamitin sulhu na MDD ba, kuma baya bisa doron dokokin kasa da kasa.

Shin Amurka ta dauki wannan mataki ne saboda rikicin Ukraine ko kuma saboda wani boyayyen muradi na ta? Shin me ye laifin Sin na kin goyon bayan wani bangare da nacewa ga neman sulhu? Za a iya cewa, Amurka na da wata manufa ta daban kamar kullum, kamar yadda ta saba neman duk wata kafa ko dalili na kuntatawa kamfanonin Sin da zummar dakile ci gaban kasar da bata mata suna a duniya.

Kasar Sin ta sha nanata cewa, bata da burin danniya ko babakere. Haka kuma kofarta a bude yake na bayyana dabarunta ga kasashe masu son koyi da ita don samun irin nata ci gaba. Don haka, kamata ya yi Amurka ta ajiye makaman yakinta kan kasar Sin, ta koyi dabarun neman ci gaban tattalin arziki da raya  al’ummominta ta hanya mafi dacewa a sabon zamani, maimakon nacewa wajen bata suna da shafa bakin fenti da kuntatawa kamfanonin kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)