Hadin gwiwar yankin Beijing-Tianjin-Hebei ya haifar da sabon ci gaba
2023-02-28 09:52:21 CMG HAUSA
Rahotanni na cewa, yanzu haka ci gaban hadin gwiwar da aka samu a birnin Beijing da yankunan dake makwabtaka da shi, yana ci gaba da samun bunkasuwa, kuma ya zama wani sabon salo na ci gaban kasar Sin, shekaru 9 ke nan bayan da kasar Sin ta kaddamar da wasu muhimman dabarun gina gungu na birnin Beijing-Tianjin-Hebei.
Wani rahoto da ofishin kididdiga na birnin Beijing ya fitar a ranar 20 ga watan Fabrariru ya nuna cewa, a shekarar 2022 GDPn shiyyar Beijing-Tianjin-Hebei ya kai kudin Sin yuan triliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 1.4, karuwar kashi 1.8 daga shekarar 2013
Tsarin masana'antu, da daidaiton rarraba albarkatu da bunkasuwar kirkire-kirkire, ba wai kawai ya taimakawa babban birnin kasar Sin mai cunkoson jama’a samun ci gaba mai inganci ba, har ma ya kawo fa'ida ga biranen Tianjin da Hebei. (Ibrahim Yaya)