logo

HAUSA

Ra’ayin shugaba Xi Jinping kan Afirka ya kara bayyana ma’anar hadewar makomar Sin da Afirka

2023-02-28 15:29:54 CMG Hausa

Kwanan baya aka gudanar da taron kolin kungiyar tarayyar Afirka (AU) karo na 36 a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da sakon taya murnar kiran taron ga kasashe gami da jama’ar Afirka baki daya. A sakon nasa, shugaba Xi ya ce, hadin-gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka mai inganci na fadada zuwa fannoni daban-daban, inda a cewarsa, yana fatan yin kokari tare da shugabannin kasashen Afirka, don kara karfafa hadin-gwiwa da mu’amala tsakanin Sin da Afirka, da zummar kafa al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya.

Akwai kyakkyawan zumunci da kamanceceniya da dama tsakanin Sin da Afirka, al’amarin da ya kara hada kan bangarorin biyu. Ya zuwa sabon zamanin da muke ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da wasu muhimman manufofi don raya dangantaka tare da kasashen Afirka, wato nuna gaskiya, da sahihanci, da kauna da kuma aminci ga kasashen Afirka. A karkashin tsarin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, gwamnatin kasar Sin ta sanar da wasu “shirye-shiryen hadin-gwiwa 10”, da “muhimman matakai 8”, gami da “muhimman ayyuka 9”, wadanda suka shafi bangarorin muhimman ababen more rayuwar al’umma, da kiwon lafiya, da inganta kwarewar al’umma da sauransu.

Shimfida hanyoyin mota, daya ne daga cikin muhimman ayyukan hadin-gwiwa da ake yi tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Wani kamfanin kasar Sin ya zuba jari gami da shimfida wata babbar hanyar mota a Nairobi, fadar mulkin kasar Kenya, mai hada cibiyar birnin da babban filin saukar jiragen sama na Jomo Kenyatta, wadda ta ratsa cibiyar kasuwanci, da babban filin wasannin motsa jiki, da babban ginin majalisar dokoki, da fadar shugaban kasa da sauran wasu muhimman wurare. Zuwa farkon watan Fabrairun bana, adadin motocin da suka wuce ta hanyar, mai tsawon kilomita 27.1, wadda aka fara amfani da ita a watan Yulin bara, ya zarce miliyan 10.

A nasa bangaren, shugaban hukumar kula da tagwayen hanyoyin Kenya, Mista Kungu Ndungu ya bayyana cewa, samar da ci gaban kasa na bukatar ingantattun hanyoyin mota dake zuwa ko’ina, kuma irin wannan hanyar mota da kamfanin kasar Sin ya shimfida a Nairobi, yana taimakawa sosai wajen saukaka zirga-zirgar al’umma da jigilar kayayyaki, al’amarin da ya cancanci babban yabo.

A wajen taron kolin kungiyar tarayyar Afirka (AU) a wannan karo, wani muhimmin batun da aka tattauna shi ne, gaggauta aikin gina yankin cinikayya maras shinge a nahiyar Afirka. Amma tun da dadewa, a wasu yankunan dake Afirka, ana fuskantar matsalar karancin ingantattun hanyoyin mota, da gadoji, da tashoshin jiragen ruwa, da na’urorin samar da ruwa da wutar lantarki da sauransu, al’amarin dake kawo babban cikas ga karfafa mu’amalar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin kasashen Afirka.

A karkashin jagorancin shawarar “ziri daya da hanya daya”, ana kara cimma tudun-dafawa a fannin inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Kawo yanzu, tsawon layukan dogon da kasar Sin ta gina a nahiyar Afirka ya zarce kilomita dubu 6, gami da hanyoyin mota masu tsawon kilomita dubu 6, da tashoshin ruwa kusan 20, da sauran wasu manyan na’urorin samar da wutar lantarki sama da 80.

A karshen watan Janairun bana, aka kaddamar da fara amfani da tashar jirgin ruwa dake yankin masana’antu na Lekki a jihar Lagos dake yankin kudancin tarayyar Najeriya. An yi hasashen cewa, tashar nan wadda ta zama babbar tasha mai zurfi ta farko a yammacin Afirka, zata samar da moriyar tattalin arziki kusan dala biliyan 360 gami da guraben ayyukan yi sama da dubu 170, al’amarin da zai taimaka sosai ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

Wani kwararre mai nazarin ilimin injiniyanci daga jami’ar Zambiya mai suna Dennis Mwaba ya ce, taimakon kasar Sin ya kara inganta mu’amala da cudanya tsakanin kasashen Afirka, da kawo babban sauki ga harkokin kasuwanci da zuba jari na Afirka, da samar da ci gaba da dunkule tattalin arzikin nahiyar Afirka baki daya.

Baya ga inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma, kiwon lafiya shi ma muhimmin bangare ne dake shaida karfafar hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

A ranar 11 ga watan Janairun bana, a yankin karkara dake kudancin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, an yi bikin kammala aikin gina babbar hedikwatar cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka, wadda kasar Sin ta bada tallafin ginawa. Wannan gagarumin aikin hadin-gwiwar Sin da Afirka, ya kasance cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa ta farko wadda ke da yanayin aiki da na gwaji na zamani a duk fadin nahiyar Afirka, abun dake da babbar ma’ana ga inganta kwarewar kasashen Afirka ta fannin kandagarkin cututtuka da sa ido gami da shawo kan annoba.

Tun da kasar Sin ta fara tura tawagar ma’aikatan jinyarta ta farko zuwa kasar Aljeriya dake arewacin nahiyar Afirka a shekara ta 1963, kawo yanzu, kungiyoyin ma’aikatan jinyar kasar Sin sun yi tattaki zuwa kasashen Afirka da yawa don gudanar da aiki. Yayin barkewar cutar Ebola a kasashen yammacin Afirka a shekara ta 2014, kasar Sin ta tura kwararrun ma’aikatan jinya sama da dubu 1 zuwa Afirka don yakar cutar tare da jama’ar wurin. Daga bisani tun barkewar annobar numfashi ta COVID-19, Sin da Afirka sun baiwa juna goyon-baya da taimako. Yayin da kasar Sin take cikin mawuyacin hali wajen dakile yaduwar annobar, kasashen Afirka sun rika ba ta goyon-baya. A yayin da annobar ta barke a kasashen Afirka, ita ma kasar Sin ta tura ma’aikatan jinya da yawa zuwa Afirka, da samar mata da kyautar alluran riga-kafin cutar, al’amarin da ya kara shaida dankon zumunci tsakanin bangarorin biyu.

Taimakawa Afirka horas da kwararru, musamman matasa, muhimmin bangare ne na daban na hadin-gwiwar Sin da Afirka. Sakamakon binciken da aka yi ya nuna cewa, zuwa shekara ta 2030, kimanin kaso 40 bisa dari na matasan duniya, ‘yan Afirka ne, ke nan matasa za su zama muhimmin jigo na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da samar da ci gaba a nahiyar Afirka. Kasashen Afirka su ma suna matukar fatan inganta kwarewar matasan su, da samar musu da cikakkun guraban ayyukan yi, don taimakawa ci gaban kasashen su.

A wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar sa za ta bada tallafin ginawa ko kuma sake farfado da wasu makarantu 10 a Afirka, da gayyatar kwararrun Afirka dubu 10 don halartar tarukan kara wa juna sani.  

Har wa yau, gwamnatin kasar Sin ta ci gaba da hada kai tare da kasashen Afirka don kafa cibiyoyin koyon sana’o’i da ake kira “Luban Workshop”, da karfafa gwiwar kamfanonin kasar Sin dake Afirka su samar da guraban ayyukan yi akalla dubu 800. Tun da aka kafa “Luban Workshop” na farko a kasar Djibouti a watan Maris din shekara ta 2019, kawo yanzu, kasar Sin ta kafa irin wadannan wuraren koyon sana’o’i sama da goma a kasashen Afirka, al’amarin da ya taimaki ci gaban harkokin bada ilimin sana’o’i a wurin. Cavins Adhill, kwararre kan batutuwan kasa da kasa daga kasar Kenya ya bayyana cewa, hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannin horas da kwararru, zai kara kyautata harkokin bada ilimi na Afirka, da horas da kwararru da yawa da ake bukata a Afirka.

A karkashin jagorancin shugabannin Sin da Afirka, babu tantama za’a kara gina al’ummomin bangarorin biyu masu kyakkyawar makoma ta bai daya, da kara taimakawa ga ci gaban hadin-gwiwar kasashe masu tasowa, da samar da karin alfanu ga al’ummar duniya baki daya. (Murtala Zhang)