Mutuncin Japan ya rube a duniya saboda shawarar da ta yanka ta zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku
2023-02-28 10:55:47 CMG HAUSA
Ran 25 ga wata, ministan tattalin arziki da masana’antu da ciniki na kasar Japan Yasutoshi Nishimura ya gudanar da taron manema labarai a birnin Iwaki na jihar Fukushima, inda ya bayyana shirin kasar na zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku. Kamar yadda masuntan wurin suka yi a baya, sun nuna matukar adawa game da hakan, tare da nuna shakku cewa, yadda gwamnatin kasar ta yanke shawarar ba tare da samun amincewa daga gare su ba, mataki ne na cin amanarsu. Abin mamaki shi ne, yayin da ‘yan jarida suka yi masa tambaya kan cewa, wane mizani ne za su yi amfani da shi wajen tabbatar cewa, ko jama'a sun yarda da shirin ko a’a, Yasutoshi Nishimura ya amsa cewa, "Babu." Lamarin da ya gamu da korafi daga jama’a.
A watan Afrilu na shekarar 2021, gwamnatin Japan ta sanar da cewa, daga barazar shekarar 2023, za ta zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku, lamarin da ya gamu da shakka da rashin yarda daga gida da waje. A watan Yuli na bara kuma, gwamnatin ta zartas da wannan shirin duk da cewa hukumar IAEA ba ta kammala aikinta na bincike a kasar ba.
Teku shi ne ginshikin dogaro na kai na kasa da kasa wajen rayuwa da bunkasuwa. A matsayinta na kasar da ta kulla yarjejeniyar martaba dokokin teku ta MDD, Japan na da nauyi da ma hakki na kiyaye muhallin teku. Amma a hakika, tun daga shekarar 2013, gwamnatin Japan ta gabatar da dabaru 5 na zubar da ruwan, amma ta yanke shawarar zuba shi a cikin teku saboda ita dabara ce mafi araha. Ba ta kuma yi la’akari cewa, ko matakin nata zai karya dokar kasa da kasa, ko ma kawo illa ga muhallin halittun teku da lafiyar bil Adama ko a’a ba. Gaskiya wannan tsarin ‘yan amshin shata ya fallasa tsananin son kai da gwamnatin Japan ke da shi. (Amina Xu)