logo

HAUSA

Sin za ta ba da gudummawa wajen tafyar da harkokin hakkin dan Adam a duniya

2023-02-28 09:43:30 CMG HAUSA

 

Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bayyana cewa, kasarsa za ta bi tafarkin raya hakkin dan Adam, tare da ba da gudummawa ga harkokin kiyaye hakkin bil Adama a duniya.

Qin ya bayyana hakan ne, a lokacin da yake jawabi ga wani babban bangare na babban taron kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 52 da ya gudana ta kafar bidiyo.

Qin ya ce, ya kamata kowace kasa ta tsaya kan tafarkin raya hakkin dan Adam da ya dace da yanayinta. Haka kuma, ya kamata dukkan bangarori su kara kaimi, da kare duk wani nau'in hakkin dan Adam, da tabbatar da daidaito da adalci a duniya, da kiyaye tattaunawa da hadin gwiwa

Qin ya kara da cewa, manufar kare hakkin bil-adama ta kasar Sin ta samu nasarori a tarihi, yayin da kasar ta bi hanyar da ta dace da zamani da kuma yanayin kasar. Yana mai jaddada cewa, kasar Sin za ta bi wannan hanya sau da kafa

Qin ya ce, kasar Sin na adawa da yunkurin yin amfani da batutuwan da suka shafi yankunan Xinjiang da Tibet, wajen neman bata sunan kasar Sin da ma dakile ci gabanta. (Ibrahim Yaya)