logo

HAUSA

Gyare-gyare sun sa zaman al'umma samun ci gaba

2023-02-28 20:30:17 CMG Hausa

Abokaina, ko kun jefa kuri'unku a babban zaben kasar Najeriya na wannan karo? Da fatan za a kammala ayyukan babban zaben lami lafiya, ta yadda za a aza harsashi na siyasa mai kyau ga ci gaban kasar Najeriya cikin shekaru masu zuwa.

A telabijin, na ga wani dan Najeriya da ya halarci babban zaben ya gaya ma manema labaru cewa, “Ya kamata mu jefa kuri'a, saboda muna bukatar wata sabuwar kasar Najeriya, da sauya abubuwa da yawa.” Maganarsa ta nuna ma'anar yin zabe, wato kawo sauye-sauye ga wata kasa, inda za a yi amfani da sabbin manufofi wajen daidaita matsalolin da ake fuskanta, da raya tattalin arziki, gami da kyautata zaman rayuwar jama'a.

Batun nan ya sa ni tunawa da wani taron da jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, mai mulki a kasar, ta gudanar da shi a birnin Beijing, a kwanakin nan, inda wani babban jigon da ake tattaunawa a kai shi ne yin gyare-gyare kan tsarin hukumomin kasar.

Abokaina da suka fahimci tsarin siyasa na kasar Sin, za su san cewa, kokarin yin kwaskwarima kan manufofi da tsarin hukumomi wata babbar manufa ce da kasar ke nacewa a kai. Cikin shekaru fiye da 70 bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar kasar Sin a shekarar 1949, an yi babbar kwaskwarima kan tsare-tsaren hukumomin kasar har sau 13, inda aka takaita wasu hukumomi da ma'aikatansu, da inganta kwarewar hukumomin gwamnati ta fuskar samar da hidimomi ga al’umma, da sanya yanayin aikin mulki ya dace da tsarin baiwa kasuwa damar yin halinta, da dai makamantansu, tare da samun nagartaccen sakamako.

Idan mun dauki aikin takaita hukumomi a matsayin misali, wata kwaskwarimar da aka yi wa hukumomin kasar Sin a shekarar 2018 ita kadai, ta sa yawan ma'aikatun gwamnatin kasar ya ragu da wasu 8. Ta wannan hanya, an daidaita tsarin hukumomi, da samun karin jami'ai masu kwarewar aiki. Ban da haka, an rage ma jama’ar kasar nauyin biyan haraji, kana sun samu sauki sosai yayin da suke gudanar da wasu ayyuka a hukumomi daban daban.

Wannan kwaskwarima ta nuna yadda gwamnatin kasar Sin ke iya sabunta tsare-tsare da kanta, inda take neman zamanintar da dabarun mulki a kai a kai, ba tare da tsoron gudanar da gyare-gyare kan hukumomin kasa kai tsaye ba, musammam da zummar tabbatar da ci gaban kasa da na zaman al’umma, da gamsar da daukacin al'ummun kasar. Ma iya cewa, dukkan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya tattalin arizki, cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, shaida ce ga yadda gyare-gyare ke haifar da ci gaban zaman al'umma.

To, tun da aikin kula da wata kasa na bukatar a yi masa kwaskwarima a kai a kai. Shin duniyarmu ita ma tana bukatar samun gyare-gyare a kan tsarinta?

Hayley Arceneaux, wata 'yar saman jannati ce, wadda ta taba rubuta cewa, “ Yayin da nake hangen duniyar Earth daga sama, na ga a karkashin abubuwa masu kyan gani, akwai wasu abubuwa marasa kyau. Misali, ko da yake dukkanmu na rayuwa kan wannan duniya, amma mutanen da aka haife su a wannan bangare na duniya, da wadanda suke zama a waccan bangare, gibin zaman rayuwarsu ya yi yawa.”

A da can, wasu kasashen yammacin duniya masu karfi sun kafa wani tsarin duniya maras adalci, ta hanyar yake-yake, da mulkin mallaka, da raba ikon mallakar yankunan duniya tsakaninsu, wanda ke ci gaba da kasancewa a duniyarmu har zuwa yanzu. Sa’an nan wasu kasashe sun dade suna rike da ra'ayin “cin nasara daga faduwar wani bangare”, saboda haka suna ta neman toshe wa kasashe masu tasowa hanyar samun ci gaba. Ganin wannan yanayin da ake ciki ne, ya sa kasar Sin ta dau niyyar kafa wata sabuwar huldar kasa da kasa, wadda ta daukaka ra'ayin hadin gwiwa da samun moriya tare, gami da gabatar da shawarar kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Ayyukan kula da harkokin kasa da kasa ma suna bukatar a yi musu gyare-gyare, kana kasar Sin na ta kokarin samar da sauye-sauye da kwaskwarima kan tsare-tsaren duniya, ta yadda al'ummar dan Adam za ta dinga samun ci gaba. (Bello Wang)