logo

HAUSA

Sin ta samu babban ci gaban sha’anin harkokin matanta

2023-02-27 20:27:51 CMG Hausa


Harkokin mata a kasar Sin ya samu zarafin ci gaba, kuma ya nuna kyakkyawan makoma a cikin shekaru 10 da suka gabata. Kasar Sin ta inganta samarwa mata kiwon lafiya da inshora, tare da taimaka musu shiga ana damawa da su a harkokin raya tattalin arziki da zaman takewa.

Misali, kiwon lafiyar mata ya ingantu sosai, inda matsakaicin tsawon rayuwar mata Sinawa ya kai shekaru 80.88 a shekarar 2022, kuma mace-macen mata yayin haihuwa ya ragu zuwa 16.1 cikin mata 100,000, tun daga shekarar 2021.

A shekarar 2009, kasar Sin ta kaddamar da shirin binciken sankarar mama da ta mahaifa kyauta, ga matan dake yankunan karkara. Zuwa shekarar 2020, shirin ya aiwatar da binciken sankarar mahaifa ga mata kimanin miliyan 130, da binciken sankarar mama ga mata miliyan 64.

Haka kuma, cikin shekaru 10 da suka gabata, rawar da mata ke takawa a fannin raya tattalin arziki da zamantakewa, na ci gaba da karuwa. Shi Liping, wadda ta yi gadon surfanin gargajiya na kabilar Miao, kuma wadda ta samu lambar yabo ta mata mafiya nagarta ta Sin, ta jagoranci mata wajen fara kasuwanci ko samun aikin yi. Tsakanin shekarar 2000 da 2008, ta tattaro kayayyakin surfanin gargajiya na kabilar Miao, kuma ta kafa wani ayarin masu surfani da kuma kamfanin kayayyakin bude ido na gargajiya na kabilar Miao, a gundumar Songtao ta Miao mai cin gashin kanta dake lardin Guizhou na kudu maso yammacin kasar Sin.

Adadin mata cikin jimilar ma’aikatan kasar Sin ya kasance sama da kaso 40 cikin shekaru 10 da suka gabata. Mata sun zama muhimmin karfi dake ingiza kirkire-kirkire da kasuwanci. Mata a kasar Sin a yanzu, su ne suka dauki kaso 55 na masu kasuwanci ta intanet. Haka kuma, a shekarar 2021, mata ne suka dauki kaso 45.8 na ma’aikata a bangaren kimiyya da fasaha.

Raya harkokin ilimi ya taimakawa mata cimma burikansu. Da taimakon shirin Spring Bud, da asusun kula da kananan yara da yara ‘yan kasa da shekaru 20 na kasar Sin, Yuzhuoma, daga jihar Tibet mai cin gashin kansa ta kudu maso yammacin kasar Sin, ta kammala karatu tun daga matakin firamare zuwa jami’a, inda ta zama sojar sama a rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin, a shekarar 2011.

Bugu da kari, an yi nasarar cike gibin dake akwai wajen karatun tilas tsakanin maza da mata a kasar Sin. Yawan dalibai mata a kwalejoji da jami’o’i a yanzu, ya zarce kaso 50. Yayin da mata ke kara samun ilimi, suna kara samun kwarin gwiwa wajen samun nasarori a rayuwa.

Cikin shekaru 10 da suka shude, mata suna kara shiga ana damawa da su wajen daukar matakai da tafiyar da harkokin kasuwanci da na demokradiyya a matakan karkara.

Kiddidiga ta nuna cewa, wakilai mata a taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta NPC, karo na 13, sun kai kaso 24.9 na jimilar wakilan majalisar, haka kuma mata mambobin majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta Sin ta CPPCC, ya kai kaso 20.4 na jimilar mambobin majalisar. Wa’adin wakilan majalisar NPC na 13 da na majalisar CPPCC na 13, ya fara ne daga shekarar 2018 zuwa 2023.Bayan zabukan mambobin majalisun biyu da aka yi a bana wato reshen jam’iyyar na kauye da kuma kwamitin kauye, kowanne kauye na da a kalla mace daya a majalisun biyu. Wato kimanin rabin mambobin majalisun, mata ne.

Inshorar kula da mata ya ci gaba da ingantuwa. A karshen shekarar 2020, adadin mata da suka shiga cikin inshorar haihuwa ya kai miliyan 103, wanda ya karu da miliyan 49.31 idan aka kwatanta da na shekarar 2010. Baya ga haka, akwai mata miliyan 650 da suke cin gajiyar inshorar kiwon lafiya.

Irin wannan kiddidiga na nuna manyan manufofin shugaba Xi, na yin kyakkyawan tasirin da ake muradi. Shugaba Xi ya shaidawa shugabannin duniya yayin wani taro kan daidaiton jinsi da karfafa gwiwar mata cewa, “dole ne mu karfafa karfin mata na taka rawa wajen raya al’ummarsu da tattalin arziki, da inganta karfinsu na daukar matakai da tafiyar da harkoki da taimaka musu wajen zama shugabanni a fannonin siyasa da kasuwanci da ilimi”.

Mata marasa lisaftuwa ne suke yin kyawawan tasiri a cikin al’umma. Misali, bayan shekaru 10 da tafiyarta sararin samaniya, a ranar 5 ga watan Yunin bara, Liu Yang, ‘yar sama jannati mace ta farko a kasar Sin, ta koma sararin samaniyar, inda ta shiga kumbon binciken sararin samaniya na kasar Sin wato Tianhe, yanzu kuma ta riga ta dawo doron duniya lami lafiya. A shekarar 2021 ne, Zhang Guimei, malamar da ta kafa makarantar sakandare ta mata zalla ta farko a kasar Sin, tare da taimakawa ‘yan mata 2,000 samun ilimin gaba da sakandare, ta samu lambar yabo ta Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, wadda ita ce lambar yabo mafi daraja ta JKS. Liu da Zhang, na daga cikin misalan matan kasar Sin a sabon zamani, wadanda ke ci gaba da himmantuwa wajen bayar da gudunmuwa domin farfado da kauyuka da yin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da kandagarki da dakile annoba da kuma bayar da jagoranci a matakan karkara.

Har yanzu da sauran rina a kaba, don haka, ci gaba da kokari tare, ita ce hanyar samun ci gaba. Sinawa mata, dake zaman tsintsiya madauriki daya, na kokarin samun ci gaba cikin ruhi mai karfi, kuma suna cimma manyan nasarori a sabon zamani. (Kande Gao)