logo

HAUSA

Jirgin saman yaki samfurin J-20 zai shiga gasar "Edelweiss Assault - 2023" ta Austria

2023-02-27 09:37:34 CMG Hausa

A yayin taron manema labaru da aka shirya a kwanan baya, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Tan Kefei ya sanar da cewa, bisa gayyatar da bangaren kasar Austria ya yi mata ne, rundunar sojin kasa ta kasar Sin za ta tura wasu sojojinta da kuma jiragen saman yaki ciki har da samfurin J-20, zuwa gasar sojojin kasa na kasa da kasa bisa jigon “Edelweiss Assault - 2023” da za a shirya a kasar Austria. (Sanusi Chen)