logo

HAUSA

Aikin gina CBD na Sin ya sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa a sabon babban birnin Masar

2023-02-27 14:05:40 CMG Hausa

Jami’an kasashen Sin da Masar sun bayyana aikin ginin cibiyar cinikayya wato CBD a sabon babban birnin kasar Masar mai tafiyar da harkokin gwamnati, a matsayin misalin samun ci gaba mai dorewa da kuma sada zumunta da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Masar.

Youssry Al Salamony, Injiniyan kamfanin Dar Al Handasah na kasar Masar, da ya tsara fasalin ginin CBD, ya ce kamfanin CSCEC na kasar Sin da ya gudanar da wannan aiki, ya taimaka wajen cimma burin samun ci gaba mai dorewa a fannin kiyaye muhalli da samar da aikin yi.

A yayin taron gabatar da rahoton kamfanin CSCEC na shekarar 2021 zuwa 2022 a birnin Cairo a ranar Asabar, Youssry Salamony ya bayyana cewa, an yi amfani da makamashi kalilan da albarkatun kasa, kana aikin ya mai da hankali ga kiyaye muhalli da tabbatar da tsaro.

A nasa bangare, mataimakin shugaban hukumar kula da zuba jari na kasar, Ahmed Abdel Raziq ya bayyana cewa, don tabbatar da samun ci gaba mai dorewa, aikin ya yi amfani da fasahohin zamani, da makamashi masu tsabta kamar hasken rana, kana an yi amfani da na’urorin daskarar da ruwa don tsimin wutar lantarki. (Zainab)