logo

HAUSA

Nazari: Wasan bidiyo wata alama ce dake nuna nasarar farfadowa daga rauni

2023-02-27 10:19:25 CMG Hausa

Wani bincike da aka gudanar a kwanakin baya a kasar Australia ya nuna cewa, wasannin bidiyo da sauran fasahohi na zamani da ake samu a galibin gidaje a fadin duniya, su na taimakawa mutanen da ke jiyyar motsa jiki koyon tsayawa har ma da sake yin tafiya.

An yi amfani da na’urar VR, da wasannin bidiyo, da na'urorin sanya ido kan ayyuka, da kwamfutocin tafi da gidanka, wajen gudanar da wannan bincike, kuma shi ne irinsa mafi girma a duniya, wanda ya shafi kusan mutane 300 masu shekaru tsakanin 18 zuwa 101 da haihuwa, wadanda ke murmurewa daga lalurar bugun jini, da raunin kwakwalwa, da faduwa da ma karaya.

An gano cewa, wadanda suka yi amfani da na'urori na zamani wajen ganin sun farfado, suna da mafi kyawun motsi, a fannin yin tafiya, da tsayawa, da kuma daidaito fiye da wadanda suka yi amfani da hanyoyin farfadowa da aka saba bi kawai.

Na’ urorin Fitbits da Xbox, da Wii da iPads, su ne aka fi amfani da su a cikin binciken, da nufin kara yin mu’amula a yayin da ake motsa jiki na sake murmurewa, da kuma ba da damar kyakkyawar alaka da likitan dake kula da irin wadannan marasa lafiya.

A cewar marubuciyar da take jagorancin aikin binciken, Dr. Leanne Hassett daga Jami'ar Sydney ta kasar Australia (UOS), wadanda suka shiga binciken sun ba da rahoton cewa, ba su ji wahalar jiyyar ba, saboda na'urorin sun samar da ayyuka masu yawa da kuma nagartattun ra'ayoyi masu amfani.

Hassett ta ce, wadannan fa'idodin na nufin marasa lafiya sun fi son ci gaba da jiyya a lokacin da kuma inda ya dace da su, tare da taimakon tsarin kiwon lafiya na zamani.

Ta kuma lura da cewa, hatta tsoffi majinyata sun rungumi fasahar, kuma sun amfana da sakamako na sabbin salon. Ta ce, wadanda suka shiga binciken suna son Fitbits. Wata mace ta bukaci ta saka shi a tsakiyar dare kafin ta shiga bayan gida, domin tabbatar da cewa, an kirga dukkan takun da ta yi.

Yayin da a baya aka gwada na'urorin zamani don amfani da su a jiyyar farfadowa ta jiki, wannan shi ne bincike mafi girma irinsa a fadin duniya.

A cewar Hassaett, wannan tsari na murmurewa daga jiyya, ya tabbatar da cewa, yana yiwuwa kuma yana kuma da dadi, ya kuma nuna cewa, za a iya amfani da shi a dukkan tsarin kulawa daban-daban, kamar bayan murmurewa daga asibiti, tare da mafi yawan tallafi daga nesa daga likitoci.

Binciken ya nuna cewa, ya dace tsare-tsaren murmurewa daga jiyya a nan gaba, su kalli har da na'urori na zamani, don inganta marasa lafiya da kuma murmurewa bayan sallama daga asibiti baki daya.