logo

HAUSA

Mutane 18 sun jikkata sanadiyyar fashewar wasu abubuwa yayin gasar hawa tsauni a Kamaru

2023-02-26 17:43:15 CMG Hausa

Mutane akalla 18 sun jikkata jiya Asabar, sanadiyyar fashewar wasu abubuwa sau 3, yayin wata gasar tseren hawa tsauni a Buea, babban birnin yankin kudu maso yammacin Kamaru dake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi.

Ministan kula da harkokin wasanni na kasar, Narcisse Mouelle Kombi, ya shaidawa manema labarai bayan ziyartar wadanda suka jikkata a asibitin Buea cewa, daya daga cikin mutanen da suka ji rauni dan wasan ne, yayin da ragowar 17 suka kasance ‘yan kallo, wadanda suke kallon gasar ta shekara da ta kunshi ‘yan wasa 600, wadda ake yi wa lakabi da Mount Cameroon Race of Hope.

‘yan aware masu neman kafa ‘yantacciyar kasa a yankuna 2 na arewa maso yamma da kudu maso yamnmacin kasar dake da rinjayen masu amfani da harshen Ingilishi, sun bayyana a kafar sada zumunta cewa, su ne ke da alhakin kai hare-haren. (Fa’iza Mustapha)