Xi Jinping ya damu da gadon al’adun kasar Sin (9) Gidajen zamanin da a kasar Sin
2023-02-25 18:46:35 CRI
Gidajen da aka haka a kan dutse na Sanmingwanyan na lardin Fujian, an gina su ne shekaru dubu 185 da suka gabata. Al’ummar Sinawa na lokacin da na rayuwa a nan. An fara kawata gidajen ne kimanin shekaru dubu 40 da suka gabata, wannan aiki a nan kasar Sin ya samu asali a wannan lokaci.
Xi Jinping yana ganin cewa, kayayyakin gargajiya na da babbar ma’ana. Ya kan tunanin dabarun samun bunkasuwa tare da kiyaye wadannan kayayyaki, kuma ya dora muhimmanci sosai kan wannan aiki. Hakan ya sa, jami’an wurare daban-daban suna mutunta kayayyakin sosai, da nacewa ga ra’ayin kiyaye kayayyakin yadda ya kamata.