Sama da jami’an tsaro dubu 530 da masu sanya ido kusan duba 146 aka tura domin sanya ido kan zaben Najeriya
2023-02-25 20:13:44 CMG Hausa
A yau Asabar 25 ga watan Fabrairu ne, aka gudanar da babban zabe a Najeriya bisa wa’adin tsawon shekaru hudu. Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC, ta tura jami’an tsaro sama da dubu 530 da suka hada da ‘yan sanda da sojoji, domin ganin an magance tashe-tashen hankulan zabe da mamaye rumfunan zabe.
Domin sanya ido kan yadda za a gudanar da zaben da bayyana sakamakon zaben, kungiyoyin kasa da kasa 33 da cibiyoyin kasashen waje da suka hada da kungiyar Tarayyar Turai(EU) da kungiyar Tarayyar Afirka(AU) da kuma kungiyar kasashen yammacin Afirka, sun aike da masu sanya ido 2113 don ganin yadda zaben zai gudana. Haka kuma, hukumar ta INEC ta baiwa mutane kusan dubu 144 cancantar zama ‘yan kallo daga kungiyoyi 196 na Najeriya, wanda ke zama babbar tawagar masu sanya ido a tarihin zaben na Najeriya. (Ibrahim)