logo

HAUSA

Dabarun Sin kan yadda za a warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa

2023-02-25 15:10:53 CMG Hausa

Ranar 24 ga wannan wata, aka cika shekara daya da barkewar rikicin Ukraine, a cikin wannan shekara, ba ma kawai rikicin ya lalata tsaro da kwanciyar hankali a nahiyar Turai ba, har ma ya haifar da rashin tabbaci a fadin duniya. A game da yadda za a daidaita matsalar, a yau Asabar ne kasar Sin ta fitar da wani rahoto mai taken “Matsayin kasar Sin kan yadda za a warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa”, wanda ya samar da dabarun kasar Sin masu hikima yayin da ake kokarin daidaita rikicin.

Idan aka waiwayi tasirin da rikicin Ukraine yake jawo wa kasashen duniya a cikin shekara daya da ta wuce, ana iya kara fahimtar daraja da ma’ana na dabarun kasar Sin, ganin irin dimbin hasarar da kasashen Rasha da Ukraine suka tabka, baya ga yadda kasashen duniya suke fama da matsalar karancin makamashi da hatsi, kana darajar kudaden kasashen duniya ta ragu matuka, sakamakon wannan rikici.

A tarihin bil Adam, an gwabza yakin duniya sau biyu, kuma darrusan da aka koya sun nuna cewa, nuna fin karfi da siyasar rukunoni da yin adawa ga juna, ba abin da suke haifarwa sai yake-yake kawai, muddin aka yi shawarwari ta hanyar siyasa, to hakika za a daidaita rikici.

Sabon rahoton da kasar Sin ta fitar ya samar da cikakkun dabarun daidaita rikicin Ukraine ta hanyar siyasa. (Jamila)