logo

HAUSA

Firaministan Sin ya bukaci a karfafa ci gaba da kuma daidaita farashin kayayyaki

2023-02-25 16:31:32 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar raya tattalin arziki, da daidaita ayyukan yi, gami da farashin kayayyaki, yana mai jaddada muhimmancin kokarin da ake na kara inganta halin da ake ciki na farfadowar tattalin arzikin kasar, da sa kaimi ga samun bunkasuwa mai inganci.

Firaminista Li ya bayyana hakan ne, a yayin ziyarar da ya kai hukumar raya kasa da yin kwaskwarima ta kasa (NDRC) da ma'aikatar kudi (MOF) a ranar Alhamis. Ya kuma jagoranci taron karawa juna sani a wannan rana.

Bayan sauraron rahoto a hukumar NDRC, Li ya yaba da muhimmiyar rawar da hukumomin raya kasa da gyare-gyare suke takawa, wajen daidaita tattalin arziki da inganta ayyukan gina manyan ayyuka da ma kayayyaki na aiki.

A yayin taron ma’aikatar kudi kuwa, Li ya ce, sassan kudi sun taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da shirin dawo da kudaden haraji, da rage haraji da kudade, da tabbatar da ingancin zaman rayuwar al’umma.

Li ya bayyana cewa, a 'yan shekarun nan, duk da kalubale masu tsanani, kasar Sin ta samu manyan nasarori na ci gaba. (Ibrahim)