logo

HAUSA

Mai da masu aikin kwadago su zama ma'aikatan da suke aiki a cikin ofis

2023-02-24 19:45:49 CMG Hausa

A cikin shirin na yau, zan kai ku tashar jiragen ruwa ta Zhoushan dake garin Ningbo na kasar Sin, don mu duba yadda ake kokarin raya fasahohin zamani a can.

Tashar Zhoushan ita ce tashar jiragen ruwa daya kacal a duniya, dake iya jigilar kayayyakin da nauyinsu ya wuce ton biliyan 1 a duk shekara. A shekarar 2022 da ta gabata, an yi jigilar kayayyakin da nauyinsu ya zarce ton biliyan 1.25 ta tashar Zhoushan, adadi mafi girma a duniya, kuma wani matsayi da tashar ta kare cikin shekaru 14 da suka gabata.(Bello Wang)