logo

HAUSA

Ana ci gaba da aikin ceto a mahakar ma'adanin kwal da ta rubta a Sin

2023-02-24 20:46:02 CMG Hausa

Mahukunta a kasar Sin sun sanar a yau Juma’a 24 ga wata cewa, ana amfani da na'urori da fasahohi na zamani, yayin da ake ci gaba da aikin ceto, sakamakon rugujewar wata mahakar ma'adinan kwal a yankin Mongoliya ta gida da ke arewacin kasar Sin.

Mahakar dake Alxa ta rubta ne da misalin karfe 1 na ranar Laraba. Kuma ya zuwa karfe 2 na yau Jumma’a, an yi nasarar ceto mutane 6 daga cikin baraguzan, yayin da aka tabbatar da mutuwar mutane 6, kana wasu 47 kuma suka bace, kamar yadda hedkwatar bayar da agajin gaggawa ta yankin ta bayyana a yayin wani taron manema labarai. (Ibrahim)