logo

HAUSA

Shugaban Zimbabwe ya bukaci Amurka ta soke takunkuman da ta sanyawa Zimbabwe ba tare da sharadi ba

2023-02-24 13:29:49 CMG Hausa

Shugaban Zimbabwe Emmerson Dambudzo Mnangagwa ya gana da jakadun kasashen ketare da wakilan kungiyoyin kasa da kasa dake Zimbabwe a fadar kasa dake Harare, babban birnin kasar. A cikin jawaninsa, Mnangagwa ya yi Allah wadai da takunkumai da suka saba dokoki da Amurka kakabawa Zimbabwe, inda ya bukaci Amurka da ta soke takunkuman ba tare da gindaya wani sharadi ba nan da nan .

Amurka ta fara kakaba takunkuman da suka saba dokoki ga Zimbabwe ne tun daga ranar 21 ga watan Disamba na shekarar 2001, fiye da shekaru 20. Takunkuman sun illata karfin ci gaban tattalin arziki da kyautata rayuwar al’ummar Zimbabwe, da sanya tarnaki kan kokarin da aka yi wajen karfafa hadin gwiwa da samun ci gaba tare a cikin yankunan kudancin Afirka. A cikin shekaru 20 da suka gabata, takunkuman sun haddasawa Zimbabwe hasarar fiye da dala biliyan 40. (Safiyah Ma)