logo

HAUSA

MOC:Galibin manyan kamfanonin kasa da kasa suna son neman bunkasuwa a kasar Sin cikin dogon lokaci

2023-02-24 14:49:40 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Shu Jueting ta bayyana a birnin Bejing a jiya Alhamis cewa, ko da yake yanzu aikin zuba jari a tsakanin kasa da kasa yana cikin mawuyacin hali, amma yawan jarin da baki ’yan kasuwa suka zuba a kasar Sin yana ta karuwa cikin kwanciyar hankali, wanda ya shaida cewa, galibin kamfanonin kasashe daban daban suna son neman bunkasuwa a kasar Sin cikin dogon lokaci.

Alkaluman da aka fitar a kwanan baya na nuna cewa, a watan Janairu na shekarar bana, yawan jarin ketare da Sin ta yi amfani da shi a zahiri ya kai yuan biliyan 127.69, wanda ya karu da kashi 14.5 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara.

Shu Jueting ta yi nuni da cewa, a kwanakin baya, biyo bayan kyautatuwar manufofi da matakan kandagarkin cutar COVID-19 na Sin, ya zuwa yanzu hedkwatocin kamfanonin kasashe daban daban da dama sun tuntubi ma’aikatar kasuwancin Sin domin neman izinin ci gaba da harkokin kasuwanci a kasar Sin. Hakan ya shaida cewa, kamfanonin ketare suna da niyyar gudanar da harkokinsu a kasar Sin, har ma suna cike da imani kan makomar kasar Sin. Bugu da kari, hakan ya sake shaida yadda kasar Sin ke zama wurin da manyan kamfanonin ketare suke son zuba jari.

Shu Jueting ta nanata cewa, ma’aikatar kasuwancin Sin za ta ci gaba da maraba da zuwan masu zuba jari daga kasashe daban daban don gudanar da hadin gwiwar cinikayya a kasar, kara zuba jari a Sin, tare da samun damamakin da ake samu sakamakon ci gaban kasar Sin. (Safiyah Ma)