logo

HAUSA

Wakilai 250 ne kungiyar ECOWAS ta tura Najeriya domin sheda zaben kasar

2023-02-24 11:24:21 CMG Hausa

A ranar Alhamis 23 ga wata, wakilan kungiyar Ecowas suka isa Najeriya domin sanya ido kan babban zaben kasar da za a fara a gobe Asabar.

Wakilan da yawansu ya kai 250 suna karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Sierra Leone Ernest Koroma.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kungiyar ta Ecowas ta bukaci mahukuntan Najeriya da su tabbatar da ganin sun yi abun da duniya za ta yaba wajen gudanar da zabukan cikin gaskiya da zaman lafiya.

A lokacin da yake jawabi yayin da yake ganawa da wakilan kugiyar a birnin Abuja shugaban hukumar gudanarwar kungiyar ta ECOWAS Omar Touray ya ce, samun nasarar zaben a Najeriya tamkar nasara ce ga dukkannin kasashen dake nahiyar Afrika.

Ya ce a kowane lokaci kasashen Afrika suna koyi ne da Najeriya a harkokin da suka shafi demokuradiyya da kuma tafiyar da harkokin shugabanci.

Mr. Omar Touray ya kuma sanar da cewa wakilan kungiyar su 250 da yanzu haka suke a tarayyar Najeriya aikin su kawai shi ne sanya idanu domin tabbatar da ganin kasar ta bi dukkannin ka’idoji da dokokin gudanar da zabuka, a don haka fatan kungiyar ta Ecowas a nan, Najeriya ta yi kokarin fitar da mara da kunya.

Ya ce muddin Najeriya ta yi abin a zo a gani, to tabbas sauran kasashen dake nahiyar za su yi koyi da ita, inda ya kara da cewa abubuwan da suka faru a kasashen Mali da Guinea da kuma Bukina Faso abun kaico ne mutuka saboda gazawarsu na gina demokuradiyya.

“Matsayin Demokuradiyya a Najeriya ba wai iya shiyyar yammacin Afrika ya tsaya ba, ya shafi dukkan kasashen dake nahiyar, saboda haka ne kungiyar ECOWAS ta nuna damuwarta sosai kan wadannan zabuka.”

Shi ma a nasa jawabin, jagoran tawagar sanya ido na kungiyar Ecowas kuma tsohon shugaban kasar Saliyo Ernest Koroma, bukatar wakilan kungiyar ya yi da su yi kokarin kiyayewa da sharudodin da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya ta shimfida, kasancewar wannan zaben ya zartar sauran zabuka zafi.

Ha’ila yau ya bukaci daukacin ’yan tawagar da kowa ya sadaukar da kansa wajen ganin Najeriya ta samu nasarar wannan zaben ba tare da cin karo da wasu matsaloli ba.

“Kowane daya daga cikin mutum 4 na ’yan kasashen dake cikin kungiyar Ecowas dan Najeriya ne domin kuwa Najeriya ba ya ga kasancewarta kasar da take karfafar tattalin arzikin kasashen, ta kuma kasance kasa daya tilo da tauraron take haskawa a nahiyar baki daya.”

Wakilan kungiyar ta Ecowas an zabo su ne daga ma’aikatun harkokin kasashen wajen na kungiyar, da hukumomin zabe da jakadun kasashen dake cikin kungiyar da kuma kungiyoyin al’umma kana da kafafe yada labarai. (Garba Abdullahi Bagwai)