logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan matsayinta na warware matsalar Ukraine a siyasance

2023-02-24 11:17:43 CMG Hausa

Yau Jumma’a ne, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da takardar bayani kan matsayin Sin na warware matsalar Ukraine a siyasance.

Bayanin ya nuna cewa, ya kamata a girmama ikon mulkin kasa da kasa, a nuna adalci wajen bin dokokin duniya, kada a dauki ma’aunai guda biyu a kan batu guda. Ya kamata a yi watsi da tunanin yakin cacar baki. A tsagaita bude wuta nan da nan, tare da kaddamar da shawarwarin shimfida zaman lafiya, wannna ita ce hanya daya tak mai dacewa wajen warware matsalar Ukraine. Haka kuma ya kamata a warware matsalar jin kai da ake fuskanta yanzu, a mara baya ga dukkan matakan da za su taimaka wajen sassauta matsalar. Ban da wannan kuma, ya kamata a ba da kariya ga fararen hula da fursunoni, a tabbatar da tsaron tashar samar da wutar lantarki bisa makamashin nukiliya, a magance amfani da makaman nukiliya, a tabbatar da jigilar hatsi yadda ya kamata. Haka zakila, ya kamata a daina sanya takunkumi daga gefe guda, a tabbatar da gudanar da aikin masana’antu da na samarwa yadda ya kamata, gami da ingiza aikin sake farfadowa bayan yaki. (Kande Gao)