logo

HAUSA

Xi Jinping Da Mai Dakinsa Sun Gana Da Sarkin Cambodia Da Mahaifiyarsa

2023-02-24 16:19:36 CMG Hausa

Yau Jumma'a shugaba Xi Jinping na kasar Sin da mai dakinsa Peng Liyuan sun gana da sarki Norodom Sihamoni na Cambodia da mahaifiyarsa Norodom Monineath Sihanouk a nan Beijing.

Xi Jinping ya yi maraba da Sarki Norodom Sihamoni da Dowager Monineath da suka zo nan birnin Beijing don duba lafiyarsu da kuma murmurewa. Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin na son yin kokari tare da Cambodia wajen kafa tsarin yin hadin gwiwa a fannoni 6, tana kuma goyon bayan Cambodia wajen raya masana’antu da aikin gona, da gaggauta raya makomar bai daya ta kasashen 2. Kana kasar Sin za ta ci gaba da mara wa kungiyar ayyuka karkashin sarkin Cambodia baya wajen kara kawo wa jama'ar Cambodia alheri.

A nasu bangaren, sarki Norodom Sihamoni da mahaifiyarsa Norodom Monineath Sihanouk sun gode wa shugaba Xi Jinping da farfesa Peng Liyuan bisa yadda suka tsara shirye-shirye masu kyau da nuna kulawa kan binciken lafiyarsu da yin hutu a kasar Sin. Cambodia ta godewa kasar Sin bisa yadda ta dade tana taimakawa Cambodia da nuna mata goyon baya. (Tasallah Yuan)